Advertisement

Responsive Advertisement

Wasu magoyan bayan abba gida gida sunfara harsashen faruwan haka?

 

Me zai faru idan NNPP da APC suka haɗe a Kano?



ASALIN HOTON,arewaupdated.com

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan hukuncin kotun ƙolin ƙasar wanda ya bai wa gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf, nasara a wata shari'a kan halascin zaɓensa.

A halin da ake ciki dai babu ga-maciji tsakanin Jagoran tafiyar siyasar Kwankwasiyya wato Rabi'u Musa Kwankwaso, da Abdullahi Umar Ganduje, shugaban riƙo na jam'iyyar APC kuma jagoran jam'iyyar a Kano.

Batun dai ya soma taso ne bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Tinubu bayan hukuncin da kotun ƙolin Najeriyar ta yanke, da ya tabbatar da halascinsa a matsayin gwamna, duk da zarge-zargen da ya sha yi a baya na cewa ana shirya wata maƙarƙashiya domin ƙwace kujerar tasa.

Kwatsam kuma sai aka ga bullar wasu rahotanni da ke cewa shugaba Bola Tinubu ya bai wa jagororin jam’iyyar ta APC umarnin su je su sasanta da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayan haka nan an ga wasu mashawartan Gwamna Abba suna sanye da huluna masu ɗauke da tambarin hular Shugaba Tinubu, har wasu ma sun kai ga sanya tutar jam’iyyar APC a ofisoshinsu.

Injiniya Buba Galadima, na cikin shugabannin jam’iyyar NNPP na Najeriyar, ya kuma yi wa BBC bayanin cewa a siyasance jam'iyyar na iya tattaunawa da kowanne ɓangare, "Yan NNPP da suka fara sanya alamun jami'iyyar APC, ƙila sun zaƙu ne na cewa a yi tafiya tare, amma wanna bai nuna cewa su ne ke riƙe da jam'iyya ko su ke riƙe da gwamnati wanda za su iya zartarwa ba'. In ji shi

Buba Galadima

Post a Comment

0 Comments