Advertisement

Responsive Advertisement

Sheikh Zakzaky Ya Aikowa Da Ƴan Gudun Hijira Na Gandi Da Tallafin Kayan Abinci

Sheikh Zakzaky Ya Aikowa Da Ƴan Gudun Hijira Na Gandi Da Tallafin Kayan Abinci

Daga, Bilal Nasir Umar Sakkwato.

Da yammacin Yau Juma'a 28 ga watan Ramadanan shekara ta 1443 daidai da 29 ga watan Afrilu shekara ta 2022 saƙon tallafin kayan abinci da Sheikh Zakzaky ya aiko ga ƴan gudun hijira na garin Gandi dake cikin ƙaramar hukumar Raɓah ta jahar Sakkwato ya isa a hannunsu. Tallafin kayan abincin da suka haɗa da Shinkafa, Taliya, Indomie, Madara, dss.

Malam Sidi Munir waƙilin ƴan'uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky na Sakkwato ne ya jagoranci kai kayan ga ƴan gudun hijirar da suka fito daga garuruwa daban-daban waɗanda hare-haren ƴan ta'adda ya shafa.

An kuma miƙa kayan ne ga Malam Bello Amadu  wanda shine yake kula da Camp ɗin ƴan gudun hijira dake garin na Gandi, haka kuma an rarraba kayan ga hakimai na kowane gari inda shi kuma Hakimi zai sadarda kayan ga jama'arsa.

Daga cikin garuruwan da ƴan gudun hijirar suka fito akwai, Taɓanni, Alikkiyo, Rakwamni, Ruwan Tsamiya, Tafkin Kwasa, dss.

Jama'ar sun yi godiya matuƙa tare da jin daɗi na wannan gudummuwar da suka samu tare da yin addu'o'i na musamman ga jagoran Harkar Musulunci a wannan nahiya Sheikh Zakzaky (H).

Post a Comment

0 Comments