Advertisement

Responsive Advertisement

MAJIGIRI YA YI ZAMA DA SHUWAGABANNIN SOCIAL MEDIA NA JAM'IYYAR PDP, NA JIHAR KATSINA BAKI DAYA

MAJIGIRI YA YI ZAMA DA SHUWAGABANNIN SOCIAL MEDIA NA JAM'IYYAR PDP, NA JIHAR KATSINA BAKI DAYA

DAGA: Cmrd Abubakar Ilya. 

Da yammacin yau Lahadi, bayan kammala taron bayyana takarar H.E Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas). Ya samu damar gudanar da wani muhimmin zama da masu amfani da kafar zamani ta soshiyal midiya.

Zaman ya samu gudana ne a karkashin shugaban kungiyar PDP soshiyal midiya ta jihar Katsina baki daya, wato Amb Nuraddeen Adam Tina da sauran Shuwagabannin kungiyar a matakin jiha da zoning.

A wajen zaman akwai wakilai na kowace karamar hukuma guda Talatin da Hudu (34 L.G Coordinators) da sauran masu rike da mukamai daga kanan hukumomi.

A lokacin da yake jawabi Hon. Majigiri, ya nuna matukar jin dadin sa da mika godiyar shi ta musamman ga jajirtattun matasan da suka halarci wannan zama. Inda ya yi godiya ta musamman bisa irin yadda suke jajircewa ba dare ba rana don kare martabar jam'iyyar PDP da kuma tashi a matsayin shi na shugaban jam'iyyar PDP na tsawon shekaru bakwai har zuwa yau da ya bayyana aniyar shi ta tsayawa takarar gwamna.

Majigiri ya tabbatarwa matasan da cewa kamar yadda aka sha wahala a tare toh da yardar Allah dadin ma idan yazo tare za asha shi. Inda ya bayyana cewa idan har akwai ranar da dama zata zo masa ya manta da wannan matasan toh kar Allah ya bashi wannan dama domin kuwa yasan alhakin su ba zai barshi ya zauna lafiya ba.

Daga karshe ya kara da jan hankalin 'ya'yan wannan kungiyar akan cewa aje aci gaba da kare mutuncin jam'iyyar PDP ba tare da cin mutuncin kowa ba. Kuma daga yau an dora Damba na fara aiki tukuru game da wannan takara da ya fito nema har Allah ya bada nasara.

Haka zalika shima Hon. Hamisu Gambo Danlawan wanda yana daya daga cikin jagororin da suka halarci wannan zama ya mika gidiyar shi ta musamman ga wannan kungiya akan irin namijin kokarin da take na kare martabar PDP da zakulu ayyukan alkairin da tayi a lokacin mulki.

Allah ya shige mana gaba. Ameen👏

Post a Comment

0 Comments