Advertisement

Responsive Advertisement

Hukumar NDLEA Ta Kama Cek Na Sama Da Naira Biliyan Ɗaya, Cocaine kilograms 10.89 A Filin Jirgin Saman Legas

Hukumar NDLEA Ta Kama Cek Na Sama Da Naira Biliyan Ɗaya, Cocaine kilograms 10.89 A Filin Jirgin Saman Legas

An kama tramadol miliyan 2.3, kwalabe na Codeine 2,919 a Kaduna

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA a  filin jirgin saman Murtala Muhammed, MMIA, Ikeja Legas sun kama cak din wasu matafiya a cikin kuɗaɗen ƙasashen waje daban-daban da adadinsu ya kai biliyan ɗaya, miliyan ɗari ɗaya da hamsin da bakwai, dubu ɗari shida da saba'in da naira ɗari hudu da sittin da tara da kuma Kobo casa'in da biyu (N1,157, 670,469.92). 

Haka kuma an kama wani da ake zargi, Oguma Richard Uchenna kan yunƙurin fitar da cak ɗin, waɗanda aka ɓoye da kyau a cikin litattafai huɗu masu kama da littafan ayyukan ilimi, zuwa kasar Burtaniya.

An gano kayayyakin kudaden da ake zargin jabun ne a ranar Laraba 27 ga watan Afrilu a rumfar da NAHCO ke fitarwa a filin jirgin sama na Legas a yayin gwajin dakon kaya na wasu kayayyaki da aka yi niyyar fitarwa zuwa Burtaniya a cikin jirgin dakon kaya (cargo). 

Cak ɗin ya nuna cewa suna da darajar kuɗi dubu ɗari biyu da tamanin da bakwai, dala ɗari shida da ashirin da uku, centi talatin da ɗaya ($287, 623.31); Dalar Canada miliyan daya da dari hudu da hamsin da shida da dari uku ($1,456,300) da miliyan ɗaya da ɗari biyu da casa’in da bakwai da ɗari takwas (1,297,800).

Hakazalika, jami’an hukumar NDLEA a filin jirgin sun daƙile yunƙurin da masu safarar miyagun ƙwayoyi suka yi na shigo da hodar iblis mai nauyin kilogiram 10.89 zuwa Najeriya ta jirgin Qatar Airways. Sun ɓoye haramtaccen ƙwayoyin ne a cikin kwalayen yara guda bakwai da aka cika a cikin wata jakar da ba mai ita daga kasar Brazil.

A daya bangaren kuma, samamen da aka kai a jihohin Kaduna, Ondo da Akwa Ibom, sun yi nasarar kame kimanin kilogiram 2,000 na Tramadol, Codeine, wiwi da Heroin. A jihar Ondo, an gano 401kg na tabar wiwi sannan an kama wasu mutane biyu: Julius Dapo mai shekaru 56 da Emeka Ikebuaku mai shekaru 32 a dajin Ipele da ke unguwar Owo a ranar Lahadi 24 ga watan Afrilu.

A wannan rana har ila yau, an kama wani mai safarar muggan kwayoyi mai suna Chigbo Chinonye, ​​mai shekaru 42, dauke da amphetamine mai nauyin kilogiram 2.5 da kuma tabar heroin mai nauyin kilogiram 0.5 a yayin da ake gudanar da bincike a kan hanyar Oron-Ibaka kan hanyarsa ta zuwa kasar Kamaru.

Ya ɓoye magungunan ta hanyar amfani da marufi na ƙasa na ƙarya.

A Kaduna, an kama kwali guda 47 na Tramadol na bogi, dauke da sachet 2,350,000, masu nauyin kilogiram 1222 a Zaria a ranar Litinin 25 ga Afrilu, yayin da aka kama wani dilan ƙwayoyi, Chinedu Asogwa a ranar 26 ga Afrilu a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, dauke da kwalabe 2919 na maganin tari codeine, wanda ya kai lita 291.9 da nauyin 396kg. 

Yayin da yake yabawa jami’an hukumar MMIA, Ondo, Akwa Ibom da kuma Kaduna na hukumar bisa kame da kwato muggan ƙwayoyi a makon da ya gabata, Shugaban Hukumar NDLEA,  Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya bukaci su da sauran ‘yan uwansu a fadin kasar nan da su kasance masu jajircewa da kuma taka tsan-tsan a yayin gudanar da ayyukan su. 

Mahmud Isa Yola

Hedikwatar NDLEA, Abuja

Lahadi 1 ga Mayu 2022

Post a Comment

0 Comments